1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsad da Prodi a mukamin sabon Firimiyan Italiya

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buxs

Wata guda bayan zaben ´yan majalisar dokoki a Italiya, a yau laraba aka yi bikin rantsad da sabon FM Romano Prodi a birnin Rom. Shugaban kasa Giorgio Napolitano ya mikawa Prodi da sauran ´ya´yan majalisar ministocinsa ta masu matsakaicin ra´ayin sauyi shahadun kama aiki. Sabuwar gwamnatin ta kunshi ministoci 25, cikin su har da tsohon FM Massimo D´Alema wanda aka ba shi mukamin ministan harkokin waje. Yayin da Tommasi Padoa tsohon dan kwamitin zartaswan babban bankin Turai, ya samu mukamin ministan tattalin arziki. Gwamnatin kawancen karkashin jagorancin Prodi na da rinjayen kujeru biyu ne kadai a majalisar dattijai. A gobe alhamis za´a gudanar da kuri´ar amincewa da gwamnati a majalisar ta dattijai. A lokacin da yake jaweabi bayan an rantsad da shi sabon FM na Italiya cewa yayi:

“Alhakin da ya rataya wuyan mu shi ne mu sake maido da wani ruhi na yarda da zumunci tsakanin al´umar Italiya. Bai kamata a rika samun hauhawar tsamari ko dambaruwar siyasa a cikin wannan kasa ba. Dole ne kuma mu bayyana manufofin mu ba tare da bata lokaci ba.“