An rantsad da Kaczynski a mukamin sabon Firimiyan Poland | Labarai | DW | 14.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsad da Kaczynski a mukamin sabon Firimiyan Poland

Shugaban Poland Lech Kaczynski ya rantsad da dan´uwan tagwaitakarsa Jaroslaw Kaczynski a mukamin sabon FM kasar. Rahotanni sun nunar da cewa bisa ga dukkan alamu a ranar laraba mai zuwa sabon FM zai fuskanci kuri´ar amincewa da shi a majalisar dokokin kasar ta Poland. A bara Jaroslaw Kacynski rikakken mai ra´ayin kishin kasa, ya ki karbar mukamin FM kasar ta Poland saboda ba ya son ya kawo wa dan´uwansa cikas a zaben shugaban kasar da aka gudanar. Jaroslaw dai shi ne shugaban jam´iyar ´yan kishin kasa wadda ta fi yawan wakilai a cikin gwamnatin hadin guiwa.