An ranstar da sabuwar Majalisar dokokin Palestinu | Labarai | DW | 18.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ranstar da sabuwar Majalisar dokokin Palestinu

Darfur

Darfur

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas ya jagoranci bukin rantsar da sabuwar majalisar doki da a ka zaba ranar 25 ga watan Janairu da ya gabata , wadda kuma kungiyar Hamas ke da rinjaye a cikin ta.

A cikin jawabin da yayi, Abbas, ya gayyaci kungiyar Hamas da ta girka sabuwar gwamnati.

Saidai ya bukaci kungiyar ta yi wasti da akidar ta, ta yakar Israela, ta kuma amince da yarjejeniyoyi da a ka rataba hannu kan su a shekarun baya tsakaninhukmar Palestinawa da Israela.

Jagoran yan majalisun dokokin Hamas,Ismael Haniyeh, wanda kuma a ke sa ran, zai hawa mukamin praminista, yayi watsi da bukatocin na Mahamud Abas.

Ya ce Hamas ba zata dakatar da kai hari ba, ga yahudawa muddun, su ka ci gaba da mamaye yankunan Palestinawa.

A karshen zaman taron, yan majalisun dokoki, sun zabi Aziz Doweik dan shekaru 52 a dunia, kuma Professa a Jami´a, a matsayin sabans hugaban majalisar.