1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rage mashawarta a fadodin hukumomin Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou/GATMay 9, 2016

A makon da ya gabata ne hukumomin Nijar suka dauki matakin dakatar da aikin dimbin masu bai wa shugaban kasar shawara da 'yan aike da ma wasu tarin masu bashi shawara da ke da mukamman ministoci.

https://p.dw.com/p/1IkXh
Niger Präsident Issoufou Mahamadou
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Calanni

A jamhuriyar Nijar wata sabuwar takaddama ce ta barke kan mahimmancin tarin mashawartan fadar shugaban kasa da ta Firaminista da ma a fadar shugaban majalisar dokoki, tsakanin 'yan rajin kare demokradiya da wasu tarin mashawartan, jim kadan bayan soke mukamansu. 'Yan rajin kare hakin dan Adam dai na cewar ga kasa mafi talauci kamar Nijar bai kamata a wuce mashawarta sama da 10 ba a fadar ta shugaban kasa. Masu sukar lamirin dai na zargin cewar wasu mashawartan kan shafe tsawon shekara ko fiye da haka ba tare da ganin shugaban kasa ba.

A makon da ya gabata ne hukumomin kolin kasar Nijar suka dauki matakin dakatar da aikin dimbin masu bai wa shugaban kasar shawara da 'yan aike da ma wasu tarin masu bashi shawara na musamman da ke da mukamman ministoci su sama da 20. Ba tun yau ba dai wasu manazarta da ma masu sharhi a kan alamura ke zargin fadodin guda uku na zartarwa da tara dimbin jamaa a matsayin mashawarta wadanda suka ce ke kwasar blus na albashi a karshen ko wane wata. Ga 'yan rajin kare hakin dan Adam da demokradiya dai ga rawar da mashawartan na fadar shugaban kasa suka taka a baya, matakin da hukumomin suka dauka ya yi dai dai kamar yadda Alhaji Mustapha kadi Oumani ya bayyana.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Hoto: Getty Images


"Kowa ya ga zubinsu da cewa kasa ba ta yi amfani da su ba. Kamar wani nauyin banza da yofi ne suke kawo wa kasa kuma idan aka dubi dokoki na kasa sun yi wa kasa nauyi, saboda hakan muna jinjina wa shugaban kasa da ya mayar da su gefe domin yawancin shawarwarin da suke bayarwa na gama mutane da rarraba kanun 'yan kasa, ko na gyaran kansu"


Sai dai ga wasu tsoffin mashawartan da aka soke aikinsu, ire-iren su Malam Abdou Lokoko mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin ilimin makarantun boko, koke-koken na 'yan gwagwarmayar kare demokradiya ba ya rasa nasaba da hasada.


"Ba kai ne ke zuwa ka ce wa shugaban kasa ba ka yi mashawarci da ni ko dan aike, shi ne ke dauka da kansa, kenan duk wanda ka ga an dauka ba bu wanda ya fado katsam a haka. A gaskiya hasada ce kawai, an dauki wane baa dauke ni ba"

Raayi dai na cigaba da bazuwa hatta ma a wuraren 'yan siyasar da tun fil azal aka sansu da labawa ga ire-iren wadannan mukamai don raba mulki. Ga Malam soumaila Amadou shugaban jamiyyar Awaywaya ba tun yau ba ma ta kamata a ce an yi watsi da tarin mashawartan:

Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta


"Tun daga waccan kokuwar ta yakin Tandja da ta wuce yawancinsu duk an dauke su ne don ka da su gaya wa gwamnati maras dadi. Ba an dauke su ba ne don su bayar da shawarar kirki. Domin da suna shawarar kamar yadda aka sani da yanzu ba zaa kai a cikin halin da muka shiga ba. Kuma yanzu haka duk albashin daya daga cikinsu yana biyan albashin malamin makaranta uku"


Duk da yake ya zuwa yanzu shugaban kasa bai kai ga nadin mukamman wasu sabbin masu bashi shawara ba ga wasu na hannun damarsa sun ce suna da yakinin a wannan karon shugaban ba zai dauki mashawarta fiye da kima ba.
Kimanin jamiyyun siyasa 53 ne suka kama wa Shugaba Issoufou Mahamadou a zaben da ya gabata, dalilin da ya sa wasu ke hasashen ko a yanzu da kyar matsalar nan ta tarin masu bashi shawara da 'yan aike ta kasa kunnowa ganin yadda majalisar ministocin ma ta kasance mai yawan mambobi