An nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro a Kongo | Labarai | DW | 18.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro a Kongo

Kimanin kwanaki 10 gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da zai gudana a Janhuriyar Demukiradiyyar Kongo, tawagar MDD a kasar MONUC a takaice ta nuna damuwa game da karuwar tashe tashen hankula a kasar. Rahotanni sun ce a yankuna da dama na kasar ana yawaita kai hare hare akan magoya bayan masu takarar kujerar shugaban kasar wato shugaba mai ci Joseph Kabila da mataimakin sa Jean-Pierre Bemba. A wasu wuraren ma an jikata mutane da dama. A karshen makon jiya a hukumance aka fara yakin nema zaben na kuri´ar da za´a kada a ranar 29 ga watannan na oktoba. Tun bayan zagaye na farko na zaben a cikin watan agusta an yi ta yin arangama tsakanin magoya bayan Kabila da na Bemba, wanda na baya bayan nan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23.