An nemi a sake kirga kuri′u a zaben Amirka | Labarai | DW | 24.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi a sake kirga kuri'u a zaben Amirka

Wata tsohuwar 'yar takarar neman shugabancin kasar a matsayin mai zaman kanta wato Jill Sten ta bukaci da a sake kidayar kuri'un zaben shugaban kasa a jihar Wisconsin da ke a Arewacin Amirka.

'Yar takarar mai ra'ayi kare muhalli ta ce ta tattara kudade miliyan daya da dubu daya na dala Amirka wadanda ake bukata domin gudanar da aikin sake bitar sakamakon zaben a jihar ta Wisconsin wacce ke zama daya daga cikin jihohin kasar ta Amirka inda aka samu karamar tazara tsakanin Donald trump da Hillary Clinton a sakamakon zaben na ranar takwas ga watan nan na Nuwamba. Kungiyar yakin neman zaben tsohuwar 'yar takarar Jill Stein ta bayyana bukatar ganin kafin a kai ga bayyana kammalallen sakamakon wanda suka ce na cike da kura-kurai an gudanar da bincike. 

Kusan ba zato ba tsammahani ne dai 'yar takarar neman shugabancin kasar ta Amirka a karkashin inuwar Democrats Hillary Clinton ta sha kayi a gaban abokin hamayarta na jam'iyyar Republican Donald Trump wannan kuwa duk da cewa ta zarce shi da kuri'u kusan miliyan biyu a zaben. Lamarin da ya safe farfado da muhawarar da ake yi kan tsarin zaben kasar ta Amirka inda ba lalle ne wanda ya fi yawan kuri'u ne ke lashe sakamakon zabe ba.