An nada Tony Blair a matsayin mai shiga tsakani | Labarai | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada Tony Blair a matsayin mai shiga tsakani

Taron kolin samo bakin zaren warware rikicin gabas ta tsakiya dake da wakilcin kasashen yamma, ya bayar da sanarwar nada tsohon faraministan Biritaniya Tony Blair, a matsayin mai shiga tsakani. Taron da aka bude a birnin Jerusselem din kasar Israela, nada wakilcin kasashe ne irin su Amurka da Russia da kungiyyar Eu da kuma Mdd.Zaman taron wakilan dake irin sa na farko,a tun bayan da kungiyyar Hamas ta karbi madafun ikon tafiyar da harkoki a zirin gaza, zai yi kokarin zakulo matakan da suka dace ne domin kawo karshen rikicin dake tsakanin kasar Israela ne da kuma yankin Palasdinawa. Ana sa ran taron zai bukaci Mr Blair kasancewa jagoran tabbatar da burin da aka sa a gaba na samar da yantacciyar kasar Palasdinu. A dai ranar larabar data gabata ne Mr Blair ya ajiye mukamin sa, bayan shekaru goma yana matsayin faraministan na Biritaniya.