1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada sabon shugaban jam'iyyar ANC

Ramatu Garba Baba
December 21, 2017

Jam'iyyar da ke mulki a Afrika ta Kudu ANC ta zabi Cyril Ramaphosa mai shekaru 68 a matsayin sabon shugabanta domin maye gurbin shugaba Jacob Zuma.

https://p.dw.com/p/2pn2t
Südafrika ANC Parteitag Ramaphosa
Hoto: Getty Images/AFP/G. Khan

Mataimakin shugaban Afirka ta Kudu ya samu nasa ta kayar da tsohuwar matar Zuma, Nkosana Dlamini-Zuma don samun gurbin jagorantar jam'iyyar da ke fama da matsaloli da a baya suka yi barazanar wargaza jam'iyyar. Manyan kalubalen da ke gaban Ramphosa su ne matsalolin cin hanci da rashawa da suka dabibaye gwamnatin kasar.