An nada sabon Firaminista a kasar Togo | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabon Firaminista a kasar Togo

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya nada babbar abokin adawarsa Yawovi Agboyibo a mukamin sabon FM. Yanzu haka dai FM zai kafa wata sabuwar gwamnatin hadinkan kasa, bayan an cimma yarjejeniyar daukar wannan mataki watan da ya gabata. Muhimman aikin dake gaban sabuwar gwamnatin sun hada da shirye shiryen gudanar da zabe na gama gari. Tun kimanin shekaru 10 da suka wuce KTT ta dakatar da bawa Togo taimakon raya kasa sannan ta gindaya mata sharadin girke sahihiyar demukiradiya kafin ta ba ta wani tallafi.