An nada Koirala a mukamin sabon Firaministan Nepal | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada Koirala a mukamin sabon Firaministan Nepal

Bayan an shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Sarki Gyanendra na Nepal, yanzu ana ganin alamun samun zaman lafiya a kasar. A halin da ake ciki Basaraken ya nada dan jam´iyar adawa Girija Koirala a mukamin FM. Wadanda suka shirya zanga-zangar nuna adawa da mulkin Basaraken ne suka ba da shawarar nada Koirala a wannan mukami. A gobe juma´a idan Allah Ya kaimu majalisar dokoki da Sarki Gyanendra ya rushe ta cikin shekara ta 2002, zata koma zamanta a Kathmandu babban birnin kasar. A dangane da canjin alkiblar siyasa da aka samu a kasar, ´yan tawaye masu ra´ayin Mawo sun yi shailar tsagaita bude wuta ta tsawon wata 3 don bawa sabuwar gwamnatin damar fara aiki cikin yanayi na lumana. Bugu da kari kuma sun bude muhimman hanyoyin motar kasar da suka rufe makonni da dama suka gabata.