An naɗa Tony Blair a matsayin mai shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An naɗa Tony Blair a matsayin mai shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya

Jim kaɗan bayan saukar Tony Blair daga karagar mulkin Britania, ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, membobi a tanttanawar kusurwa 4, a game da rikicin gabas ta tsakiya, wato Amurika, Russia , Majalisar Ɗinkin Dunia da ƙungiyar gamayya turai, su ka naɗa shi a matsayin wakilin su na mussamman wanda zai jagoranci wannan tantanawar shiga tsakani.

Shugaban hukumar Palestinawa Abbas da Praministan Isra´ila,Ehud olmert, sun yi lale marhabin da wannan saban muƙami na Tony Blair, wanda su ka yi wa kyaukyawar shaida, tare da kwaɗayin zai taka rawar gani wajen lalubo hanyoyin warware baddaƙalar da ke wakana tsakanin Isra´ila da Plaestinu.

Ƙasashe da ƙungiyoyin da su ka ɗorawa Tony Blair wannan yauni, sun buƙaci ya aiki kafaɗa da kafaɗa da shugaban hukumar palestinawa, domin shata iyakokin kasar Palestinu.

Babban burin da a ka sa gaba, shine girka ƙasashe 2 masu, maƙwabtaka da juna, wato Isra´ila da Palestinu, wanda za su zama cikin kwanciyar hankali da lumana.