An naɗa sabon shugaban mujami′ar Lutheran | Zamantakewa | DW | 26.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An naɗa sabon shugaban mujami'ar Lutheran

Bapalisɗine ya kama ragamar shugabancin Lutheran

default

Sabon shugaban Lutheran, Munib Younan.

An naɗa wani Bapalisɗine a matsayin Shugaban Mujama'ar Lutheran da aka fi sani da Lutheran World Federation.

A yayin babban taron mujami'ar karo na goma sha ɗaya da yanzu haka ke gudana a Jamus ne aka zaɓi Munib A. Younan na reshen mujami'ar na Jordan da ke Jerusalam a matsayin shugabanta, bayan da ya sami ƙuri'u 300 daga cikin 418 na wakilan mujami'ar da ke sassa daban -daban na duniya.

Yuonan mai shekaru 59 a duniya, shi ne zai gaji Bishop Mark S. Hanson na reshen mujami'ar da ke Amirka da ya shafe shekaru bakwai yana riƙe da wannan muƙami.

NO FLASH Elfte Vollversammlung des Lutherischen Weltbundes in Stuttgart 2010

Taron mujami'ar Lutheran a birnin Stuttgart.

Ana ganin naɗa Bapalasdine a matsayin shugaban wannan mujami'a da ke da wakilai 145 daga ƙasashe 79 na duniya, a matsayin wani yunƙuri na tabbatar da ganin cewa batutuwan da suka shafi kiristoci a yankin Gabas ta Tsakiya su ne a kan gaba.

A jawabin da ya gabatar wa taron, Sabon shugaban, Younan Munib ya ce za su ci gaba da nuna adawa ga masu tsanantawa a addini da ƙyamar baƙi da Yahudawa da kuma addinin musulunci.

Haka kuma ya ce ba zai mance da rikicin da ke faruwa a ƙasarsa ba, in da yake fatan za a samu fahimtar juna tsakanin Palasɗinawa da Isra'ila. Ya kuma bayyana yaƙinin cewa tattaunawa ita ce abu mafi muhimmanci wajen samar da maslaha a zaman doya da manja da ake tsakanin Palasɗinawa da Isra'ila. Ya ce:" Mujami'ar Lutheran za ta taka muhimmiyar rawa a tattaunawa tsakanin Musulmi da Kirista ta yadda mu za mu fahimci musulunci haka kuma suma musulmi za su fahimci addinin Kirista, wanda ta haka ne za mu haɗa kai wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya.

Sannan yayi fatan duk wata tattaunawa da za a yi ba a fatar baki kawai za ta tsaya ba, za ta zamo wani ginshiki na samar da zaman lafiya da fahimta tsakanin ɓangarorin biyu.

Flash-Galerie Elfte Vollversammlung des Lutherischen Weltbundes in Stuttgart 2010

Wasu manyan jami'ai na Mujami'ar Lutheran.

Dangane da batutuwan da ake tattaunawa a taron da ke gudana a Stuttgart kuwa, Bishop Yuonan ya ce batun adalci ga kowa shine mahimmin abin da suka fi mayar da hankali a kai. "Burinmu shi ne kula da kowane ɗan adam ba tare da la'akari da ƙabilanci ko siyasa ko addini ko kuma bambancin jinsi ba inji Younan. Muna gudanar da ayyukan al'umma a Afirka da Asiya da sauran ɓangarorin duniya. A ko da yaushe adalci shi ne abu na farko da muke la'akari da shi, ba wai adalci a siyasance kaɗai ba har ma adalci ga mata a mujami'u da cikin al'umma, da adalci ga waɗanda ake safararsu da masu gudun hijira. Waɗannan abubuwa su ne manyan batutuwan da ake tattaunawa a wannan taro.

Bishop Younan shi ne malamin mujami'a na farko da ya fara fassara wani muhimmin bayani na wannan mujami'a zuwa harshen Larabci. kafin wannan naɗi, shi ne mataimakin shugaban mujami'ar kuma shugaban sassan mujami'ar da ke Yankin Gabas ta Tsakiya, sannan yana ɗaya daga cikin wakilan kwamitin ƙasa da ƙasa na kiristoci da ke birnin Ƙudus.

Mawallafiya: Hani Umar Sani

Edita: Halima Balaraba Abbas