An naɗa saban sarkin musulmi a Nigeria | Labarai | DW | 02.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An naɗa saban sarkin musulmi a Nigeria

Kwanaki 5 bayan rasuwar mai Daraja Sarkin Musulmi El Haji Muhamadu Macciɗo, hukumomin Nigeria, sun naɗa Kalan Muhamadu Sa´ad Abubakar na 3, a matsayin magajin sa.

Sakataran gwamnatin Jihar Sokoto,Maigari Dingyaɗi, da ya bayyana wannan sanarwa ya ce saban sarkin ya samu mubai´a daga gidajen sarautar baki ɗaya.

Saban sarkin musulmi na 20 Muhamadu Sa´ad Abubabakar na 3 na matsayin ƙane ,ga mirganyi Muhamadu Macciɗo.