1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An naɗa saban sarkin musulmi a Nigeria

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/BudZ

Kwanaki 5 bayan rasuwar mai Daraja Sarkin Musulmi El Haji Muhamadu Macciɗo, hukumomin Nigeria, sun naɗa Kalan Muhamadu Sa´ad Abubakar na 3, a matsayin magajin sa.

Sakataran gwamnatin Jihar Sokoto,Maigari Dingyaɗi, da ya bayyana wannan sanarwa ya ce saban sarkin ya samu mubai´a daga gidajen sarautar baki ɗaya.

Saban sarkin musulmi na 20 Muhamadu Sa´ad Abubabakar na 3 na matsayin ƙane ,ga mirganyi Muhamadu Macciɗo.