An mayarda Sharon dakin tiyata karo na 3 cikin saoi 48 | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An mayarda Sharon dakin tiyata karo na 3 cikin saoi 48

Rahotanni daga Israila sunce an sake mayarda Prime minista Ariel Sharon dakin tiyata karo na uku cikin saoi 48,bayan wani bincike da akayiwa kwakwalwarsa a yau da ya nuna cewa har yanzu jini na kwarara cikin kwakwalwartasa.

A jiya ne likitocin suka bada rahoton samun nasarar dakatar da zubar jinin bayan tiyata na saoi da dama.

Likitocin asibitin Hadassa inda yake kwance sunce da kyar ne ya koma bakin aikinsa idan ma har ya rayu.