An mayar da Charles Taylor a kotun Majalisar Dinkin Dunia ta birnin Hague | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An mayar da Charles Taylor a kotun Majalisar Dinkin Dunia ta birnin Hague

Yau ne kotun Siera Leone ,ta ka ɗauki tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, zuwa kotun Majalisar Ɗinkin Dunia, ta birnin Hague, ko kuma La Haye, domin yi masa sharia´a.

A na zargin Charles Taylor da leffika guda 11 daidai, a yaƙin bassasar da ya ɓarke a ƙasar Siera Leone, daga shekara ta 1991 zuwa 2002, ta hanyar bada tallafi ga yan tawayen Ruf.

Tun watan Maris da ya gabata, a ka capke Charles Taylor daga Nigeria, a yayin da ya ke kan hanyar sa, ta tserewa, a ka kuma, damƙa shi, ga kotun Freetown a ƙasar Sirea Leone.

Wannan kotu, ta buƙaci a maida shari´ar zuwa kotun ƙasar Holland, a dalili da mattakan tsaro.

A satin da ya gabata, ƙasar Britania ta bayyana amincewa da karbar Charles Taylor, bayan hukuncin da kotun za ta yanke masa