An kwashe dare biyu a jere ana fama da boren matasa a Paris | Labarai | DW | 31.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwashe dare biyu a jere ana fama da boren matasa a Paris

A dare na biyu a jere an yi arangama a unguwanni biyu dake wajen birnin Paris. Rahotanni sun nunar da cewa wasu matasa a wadannan unguwannin sun cunnawa akalla motoci 10 wuta sannan daga bisani suka yi taho mugama da ´yan sanda, inda suka jiwa jami´an tsaro 4 rauni. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar an yi wannan arangama ce a unguwannin Clichy-sous-Bois da Montfermeil dake arewacin babban birnin na Faransa. A cikin watan oktoban bara matasa musamman a unguwannin baki ´yan ci rani dake fadin kasar ta Faransa sun kwashe makonni da dama suna yi ta bore.