1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantad da Saddam Hussein a asibiti.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupS

Babban mai ɗaukaka ƙarar jama’a a shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussein, ya ce an kai tsohon shugaban a asibiti, saboda rashin lafiyar da yake yi, sakamakon yajin cin abincin da ya fara tun ran 7 ga wannan watan. A gobe ne dai za a ci gaba da shari’ar Saddam Hussein ɗin a birnin Bagadaza, amma jami’in kotun ya ce Saddam ba zai iya hallara ba. Ana dai yi wa Saddam Hussein da manyan jami’ansa shari’a ne saboda zargin da ake yi musu na yi wa wasu ’yan ɗariƙar shi’iti, su 148, kisan gilla a cikin shekarar 1982. Saddam da jami’ansa guda uku na yajin cin abincin ne, don nuna adawarsu ga yadda ake tafiyar da shari’arsu a kotun da kuma rashin isasshen tsaron da kotun ke bai wa lauyoyinsu. Tuni dai, an yi wa lauyoyin Saddam ɗin guda uku kisan gilla.