1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwace gidajen tsohuwar ministar mai

Yusuf Bala Nayaya
February 28, 2018

Kotun a Legas ta kwace wasu maka-maka gidaje biyu da a ka ginasu da makudan miliyoyin dalar Amirka wadanda ke zama mallakar tsohuwar ministar mai a Najeriya, wacce ma ke fiskantar tuhuma a Birtaniya.

https://p.dw.com/p/2tUB0
Österreich Wien 166. OPEC Konferenz
Diezani na fiskantar tuhuma ta cin hanci da rashawa a gida da wajeHoto: picture-alliance/dpa/H. Pfarrhofer

Diezani Alison-Madueke da ke zama mace ta farko da ta shugabanci kungiyar kasasahe masu fitar da albarkatun mai ta OPEC ta yi aiki karkashin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan har zuwa 2015.

Ita dai Mrs. Alison-Madueke na fiskantar tarin tuhume-tuhume na badakalar cin hanci da rashawa a ciki da wajen kasar ta Najeriya ciki kuwa har da a Birtaniya inda a watan Oktoba na 2015 a ka kamata a birnin London bayan da Birtaniya ta kaddamar da binciken kasa da kasa a kanta.