An kusa warware rikicin nukiliyar kasashen Iran da Nkorea | Labarai | DW | 08.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kusa warware rikicin nukiliyar kasashen Iran da Nkorea

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato Mohd El baradei yaci alwashin cewa nan bada dadewa ba hukumar sa zata samo bakin warware rikicin dake tsakanin ta da kasashen iran da Koriya ta arewa a game da makaman nukiliya.

El Baradei dai ya fadi hakan ne jim kadan da saukar sa a birnin Oslo, inda aka shirya bawa hukumarsa ta IAEA dashi kansa kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekara ta 2005.

Dan salin kasar Masar, El Baradei ya kara da cewa yana fata nan bada dadewa ba kasar Iran zata koma teburin tattauna hanyoyin warware wannan takaddama a tsakanin su da masu shiga tsakani, wato kasashe uku na cikin kungiyyar Eu.

Game kuwa da Koriya ta arewa, Shugaban hukumar ta IAEA cewa yayi an samu ci gaba a kokarin da ake na warware takaddamar dake akwai game da makaman nukiliyar.