An kusa cimma yarjejeniya a taron kolin kungiyar WTO | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kusa cimma yarjejeniya a taron kolin kungiyar WTO

Bisa ga alamu mahalarta taron kolin kungiyar cinikaiya ta duniya WTO a Hongkong sun kusa cimma yarjejeniya akan wani daftarin sanarwar bayan taro don kawo karshen tallafin da ake bawa kayan amfanin gona da ake sayarwa ketare kafin shekara ta 2013. Daftarin sanarwar bayan taron ya tanadi ba kasashe matalauta shigar da akalla kayaki kimanin kashi 97 cikin 100 ba tare da sun biya kudin kwastan ba. Hakazalika daftarin ya ba da shawarar sanya 30 ga watan afrilun shekara ta 2006 ta zama rana ta karshe da za´a kammala dukkan ka´idojin dake kunshe cikin yarjejeniyar ciniki ta birnin Doha. Rahotanni daga zauren taron sun ce kungiyar G20 ta kasashe masu tasowa da kuma tarayyar Turai sun ce a shirye suke su amince da yarjejeniyar da aka cimma. A kuma halin da ake ciki masu zanga-zangar nuna adawa da hadakar manufofin kasuwancin duniya na ci-gaba da arangama da ´yan sanda a kusa da zauren taron wanda za´a kammala a yau lahadi.