1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Osinbajo ya sauke Lawal Daura

Zainab Mohammed Abubakar
August 7, 2018

Mukaddashin shugaban Najeriya ya kori shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya ta DSS Lawal Musa Daura

https://p.dw.com/p/32kYo
Nigeria Vizepräsident Yemi Osinbajo
Hoto: Novo Isioro

Kakakin mukaddashin shugaban Najeriya ya sanar ta shafinsa na Twitter cewar, an kori shugaban hukumar jami'an tsaro na farin kaya ta DSS Lawal Musa Daura.

Kakakin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce an sauke shugaban hukumar Lawal Daura daga mukaminsa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai na hutun kwanaki 10 a wajen kasar.