An koma tebrin shawara tsakanin yan tawaye da gwamnatin Uganda | Labarai | DW | 15.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tebrin shawara tsakanin yan tawaye da gwamnatin Uganda

An koma tebrin shawarwari tsakanin gwamnati da yan tawayen LRA na Uganda, a birnin Juba na kasar Sudan.

Ranar 9 ga watan da mu ke ciki ne, taron ya watse baran-baran, bayan kasa cimma daidaito.

Ranar asabar din da ta wuce, rundunar gwamnati ta bayana kashe daya, daga magabatan kungiyar LRA, Raska Lukwiya, wanda shima kotun kasa da kasa, ta Majalisar Dinkin Dunia ke nema ruwa jallo.

Wannan kissa, ga alamu zai hana ruwa gudu, a cikin tantanawar.

Tun shekaru 18 da su gabata kungiyar tawayen LRA ta kudurci kiffar ga shugaban kasar Uganda, Yuweri Musseveni.

Rikicin tsakanin dakarun 2, ya hadasa mutuwar dubunan mutane, a yayin da kusan milion 2, su ka shiga halin gudun hijira.