An koma tebrin shawara tsakanin Iran da Russia | Labarai | DW | 14.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tebrin shawara tsakanin Iran da Russia

An koma tebrin shawar tsakanin tawagogin Rasha da na Iran, a ci gaba da neman hanyoyin warware rikicin nuklear, Iran da a halin yanzu, ke tsakiyar mahaurori a manyan ƙasashe dunia.

ƙasar Rasha, har yanzu, na tasaye kan bakan ta, na warawre wannan rikici, cikin ta hanyar shawarwari, saɓanin Amurika da ƙungiyar gamaya turai, da su ka fi buƙatar komotin sulhu, na majilisar ɗinkin Dunia, ya ɗauki mattakan hukunta Iran.

Shawara da hukumomin Rasha, su ka gabatar, na buƙatar Iran, ta girka tashoshin sarrafa makamashin nuklea, a Rasha, don hidda shakun da ake, na kar ta yi amfani da wannan dama, domin ƙera makaman nuklea.

An koma tebrin shawarwarin, a yayin da nan gaba a yau, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, zai zaman taro, a kan rikicin na Iran.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne, hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea, ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta shigar da ƙaran Iran, gaban komitin.