An koma shawarwari a birnin Abuja don sulhunta rikicin yankin Dafur | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma shawarwari a birnin Abuja don sulhunta rikicin yankin Dafur

A yau ne ake komawa teburin shawarwari a birnin Abuja a zagaye na bakwai na sasanta rikicin yankin Dafur tsakanin gwamnatin Sudan da yan tawaye. Shugabannin kungiyoyin yan tawayen sun yi alkawarin bada cikakken goyon baya domin cimma nasarar shawarwarin. Kakakin kungiyar gamaiyar Afrika wadda ke shiga tsakanin don sasanta rikicin, yace tuni kungiyoyin yan tawayen suka isa Abuja domin halartar taron. Taruka shida da aka gudanar a baya basu kai ga cimma yarjejeniya ba musamman akan batutuwan da suka shafi rabon madafan iko da shaánin tsaro da kuma rabon arzikin kasa wadanda sune jigon rikicin da ake fuskanta.