An koma shariar Saddam ba tare da Saddam ko lauyoyinsa ba | Labarai | DW | 01.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma shariar Saddam ba tare da Saddam ko lauyoyinsa ba

An koma sauraron shariar tsohon shugaban kasar Iraq,Saddam Hussein da mukarrabansa a yau laraba amma ba tare da Saddam ko lauyoyinsa sun baiyana a gaban kotun ba.

Uku ne kadai daga cikin wadanda ake tuhuma suka baiyana gaban kotum,bayan kusan saoi uku na tsaiko da aka samu kafin fara shariar.

Alkalin kotun yace,duk da cewa Saddam da sauran mukarrabansa 5 basu zo kotun ba a yau,zai ci gaba da sauraron shariar.

Tun da farko a yau lauya mai kare Saddam Khalil al-Dulaimi,ya fadawa kanfanin dillancin labari na Reuters a Amman cewa,babban alkalin kotun dake sauraron shariar saddam din wato,Abdel Rahman baya nuna adalci wajen Shariar,inda yace yana kokarin gagguata yanke hukunci ne akan Saddam da mukarrabansa.