An koma sauraron shariar Saddam Hussein | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma sauraron shariar Saddam Hussein

A yau aka koma kotu domin ci gaba da sauraron shariar tsohon shugaban kasar Iraqi,Saddam Hussein,inda ake sa ran shaidu zasu baiyana karo na farko cikin shariar tasa.

Bayan yan gajerun lokuta da aka saurari shariar kafin janyewarsu har sau biyu,jamian kasar sunce,suna fatar kwanaki hudu da zaayi ana sauraron karar zai baiwa shaidu 10 da ake da su damar baiyana gaban kotun kafin a sake dageta don bada damar gudanar da zabe na ranar 15 ga wannan wata da muke ciki.

Akalla shaidu 3 ake sa ran zasu baiyana a yau litinin domin bada shaida game da kisan gilla na mutane 148 a garin Dujail a 1982.