1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An koka da rashin samun nasarar yaki da ta´addanci a duniya.

Kwamitin yaki da ta´addanci da MDD ta kafa ya fid da wani rahoto, inda a ciki yayi korafi game da rashin tabuka wani abin a zo a gani a yakin da ake yi da ayyukan ta´addanci a duniya.

Ko shakka babu babban abin da gamaiyar kasa da kasa ta sa a gaba tun bayan hare-haren ta´addancin ran 11 ga watan satumban shekara ta 2001, shi ne yaki da ´yan ta´adda na kasa da kasa. To amma matakan yin gaban kanta da Amirka ta dauka a rikicin Iraqi da bambamce bambamcen ra´ayi a tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai da kuma rashin jituwa a tsakanin kasashen nahiyar Asiya na kawo babban cikas ga samun nasarar cimma manufar da aka sa a gaba.

Wani rahoto da MDD ta bayar yayi nuni da cewa har yanzu gamaiyar kasashen duniya ba ta cimma wani abin a zo a gani ba a yakin da take yi da ta´addanci. Shugaban kwamitin yaki da ta´addanci na MDD Heraldo Munoz dan kasar Chile ya ce har yanzu ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da takunkuman MDD akan kungiyoyin Taliban da Al-Qaida. Mista Munoz ya ce saboda haka yanzu magoya bayan Osama Bin Laden na kara bazuwa kuma duk da dora hannu da aka yi kann ajiyar ta a bankunan, har yanzu kungiyar Al-Qaida ba ta fuskantar wata matsala ta rashin kudi, domin tuni ta rigaya ta janye kudadenta daga bankuna, tun kafin a dauki wannan mataki kanta.

Mista Munoz ya ce ´ya´yan kungiyar Al-Qaida na amfani da tsarin ajiyar kudi irin na kasashen Larabawa, abin da ke da wuya gamaiyar kasa da kasa ta iya dora hannunta a kai. Haka zalika kungiyar na samun taimakon kudi daga wasu kungiyoyin ba da agaji a yankin GTT da ma a wasu wuraren a yankin Asiya. Wata kafar samun kudin kungiyar Al-Qaida da kungiyar Taliban ita ce fasakaurin miyagun kwayoyi, inda ake da wata alaka mai karfi tsakanin kungiyoyin da kuma masu fataucin kwayoyin. Alal misali ´yan sumogar na biyan ´ya´yan Taliban makudan kudade na kariya, sannan a wani lokacin kuma suna musayar muggan kwayoyin ne da makamai.

Ko da yake an san da haka, amma gamaiyar kasa da kasa ta kasa yin wani abin kirki wajen fatattakar ´yan ta´addan.

Duk da haka dai mista Munoz yayi kira da a kara matsa kaimi wajen yaki da ta´addanci, sannan a karshen wannan shekara ya ce zai fid da jerin sunayen kasashen da ba sa ba da taimakon da ya kamata ga aikin yaki da ta´addancin.
 • Kwanan wata 15.11.2003
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnb
 • Kwanan wata 15.11.2003
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnb