1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kira ga turai data taimakawa Darfur

Zainab MohammedDecember 8, 2007
https://p.dw.com/p/CZCh

Prime ministan Spain yayi kira ga kasashen turai dana Afrika dasu aikin hadin gwiwa wajen bunkasa harkokin ilimi da samar da ayyukan yi da wasu kayayyakin more rayuwa,domin kare bakin haure dake kutsawa kasashen turai 27,daga nahiyar ta Afrika .Jose Luiz Zapatero,wanda yayi wannan kiran a jawabinsa wa taron hadin gwiwar turai da Afrika dake gudana a Lisbon,yace kwararan bakin haure ,shine matsalar da suka gaza magancewa.Shi kuwa a bangarensa lauyan kasar Sudan mai fafutukan kare hakkin farar hula Salih Osman kira yayi ga kasashen turan dasu ceci alummomin Darfur.

"Turai nada babban alhaki na shiga tsakani tare da aikewa da sojojin ta domin kare rayukan bayin Allah dake cigaba da mutuwa a kowace rana.Domin ta aike da dakarun ta zuwa Kosovo domin taimakawa fararen hula,ba tare da amincewar komitin sulhun mdd,me zai hanata turawa Darfur dake kusa da ita.