An kira ga shugannin EU da su amince da manufar bai daya kan muhalli | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kira ga shugannin EU da su amince da manufar bai daya kan muhalli

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga takwarorin ta na KTT EU da su amince da wata manufa ta bai daya akan muhalli da kare kewayen dan Adam. Ta ce ya kamata kungiyar EU ta zama jagora a batutuwan da suka shafi kare muhalli. Misis Merkel ta yi wannan kira ne kwana daya gabanin taron kolin da shugabannin kungiyar mai membobi kasashe 27 zasu yi a birnin Brussels a karkashin jagorancin Jamus. A cikin wata wasika da suak aikewa Merkel, manyan manyan kungiyoyin kare muhalli sun jaddada bukatar dake akwai ta cimma wata yarjejeniya akan shawarar da hukumar kungiyar EU ta bayar na rage fid da iskar CO2 da kashi 20 cikin 100 kafin shekara ta 2020. To sai dai hadaddiyar kungiyar ´yan kasuwar Jamus sun yi kashedi game da kulla wata yarjejeniya mai tsauri wadda zata iya yi janyo koma baya ga harkar kasuwanci.