An kebe kwanaki 3 domin makoki a Nigeria | Labarai | DW | 30.10.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kebe kwanaki 3 domin makoki a Nigeria

Dubban mutane cikin hawaye sunyi dafifi zuwa fadar marigayi Sultan Sokoto Alh Mohammadu Maccido ,wanda ya kasance daya daga cikin mutane 95 da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin sama jiya a Abujan tarayyar Nigeria.

Tuni dai gwamnati ta sanar da soke ayyukan jirgin Boeinf 737,mallakar kamfanin ADC,hatsarin da aka danganta da watsi da matukin jirgin da umurnin da aka bashi na kada ya tashi sakamakon ruwan sama da iska.

Ministan kula da harkokin Sufurin sama,Babalola Borishade ya fadawa taron manema labaru yau cewa,yanzu haka ana jinyar wadanda suka tsira da rayukansu,ayayinda aka samu daman ciro gawawwakin mutane 96 da suka rasa rayukansu.A yau ne dai shugaba Olusegun Obasanjo wanda ke kan hanyarsa zuwa Sokkoto,ya sanar da ware ranakku uku na zaman makokin wadanda suka rasa rayukansu a wannan hadari na jiya da rana.

 • Kwanan wata 30.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu52
 • Kwanan wata 30.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu52