1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen yajin aikin maaikata a Afrika ta kudu

June 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuHi

An kawo karshen yajin aikin maaikata mafi tsawo tun bayan karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afrika ta kudu.

Kungiyoyin kodago dake wakiltar dubun dubatar maiakatan kasar sunce dukkanin membobinsu zasu koma bakin aikinsu.

Gamaiyar kungiyoyin kodagon sun amince da tayin da gwamnati ta yi maus na karin kashi 7.5 na labashinsu.

Tunda farko dai sun nemi karin kashi 9 ne cikin dari yayinda gwamnatin kuma anata bangare tace tsaya kann kashi 6 cikin dari.

Anan ganin kawo karshen yajin aikin zai sassauta matsain lamba da shugaba Thabo Mbeki wanda yanzu haka jamiyarsa dake mulkin kasar ke gudanar da babban taronta cikin sabanin raayoyi.