An kawo karshen tarzoma data barke a gidan yarin Kabul
March 1, 2006Mahukunta a kasar Afghanistan sun samu sukunin shawo kann tarzomar data barke a cikin gidan yarin birnin Kabul.
Tarzomar da aka shafe kwanaki kusan hudu ba tare da shawo kann ta ba, ya zuwa yanzu bayanai sun nunar da cewa tayi asarar rayuka a kalla 6 da jikkata wasu 40.
A cewar mataimakin ministan shari´a na kasar tuni aka canzawa fursunonin da ake zargi nada hannu a cikin wannan tarzoma gurin zama.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa daga cikin fursunoni 1, 300 da ake zargi nada hannu a cikin wannan tarzoma guda dari 3 daga cikin su yan kungiyyar taliban ne da kuma Alqeeda.
Fursunonin dai na zargin gwamnati ne da ci gaba da tsare su ba tare da gurfanar dasu a gaban kuliya ba, kana a hannu daya kuma da nuna fushin su a game da dokar saka su sanya kaya na bai daya.