1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen taron kasashen kungiyar APEC a Koriya Ta Kudu

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKR

A karshen taron kolin da suka yi a birnin Busan na KTK, kasashe membobin kungiyar habaka tattalin arzikin yankin Asiya da Pacifik APEC sun yi kira da a samu wani ci-gaba a taron kungiyar cinikaiya ta duniya WTO da zai gudana a Hongkong cikin watan desamba. Ko da yake ba´a ambaci sunan KTT a cikin sanarwar bayan taron ba amma an soki lamirin ta da cewa suna kawo cikas ga tattaunawar da za´a yi. Saboda haka an yi kira ga dukkan memebobin kungiyar ta WTO da su nuna sassauci don samun sakunin warware takaddamar da ake yi akan tallafin da ake bawa manoma. A cikin wata sanarwa kuma kasashen kungiyar ta APEC sun yi tir da ayyukan ta´addanci sannan kuma sun kira da a karfafa ba juna hadin kai a yakin da ake yi da yaduwar masassarar tsuntsaye. Australiya ta ba da sanarwa ware dala miliyan 70 a wani mataki na yaki da yaduwar cutar ta murar tsuntsaye.