An kawo karshen taron akan yaduwar kananan makamai ba da wani sakamako ba | Labarai | DW | 08.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo karshen taron akan yaduwar kananan makamai ba da wani sakamako ba

Ba tare da an ba sanarwar bayan taro ba an kammala babban taron MDD akan yaki da yaduwar kananan makamai a duniya. Jerin kasashe kamar Amirka da Rasha da Indiya da Pakistan da Iran da kuma Isra´ila sun ce ba zasu yarda da wani shirin hadin guiwa na yaki da cinikin kanana makamai ba a barauniyar hanya ba. Alkalumman da MDD ta bayar sun nunar da cewa a kowace shekara ana halaka mutane kimanin dubu 500 da kananan makamai kamar bindigogi da dai sauran su. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nuna rashin jin dadin sa game da sakamakon taron. Ministan ya ce gwamnatin tarayyar Jamus da kawayenta na KTT sun yi fatan samun wani sakamako na a zo a gani a wannan taro.