An kawo ƙarshen kokawar madafan iko a Ukrain | Labarai | DW | 27.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo ƙarshen kokawar madafan iko a Ukrain

Shugaban ƙasar Ukrain Viktor Yushenko ya sanar da kawo ƙarshen kokawar madafan iko tsakanin sa da P/M Viktor Yanukovic, bayan da shugabanin biyu suka amince da ranar 30 ga watan Satumba domin gudanar da sabon zaɓe. Yarjejeniyar ta zo ne bayan tattaunawa ta tsawon saói da shugabanin suka gudanar a Kiev babban birnin ƙasar. Dambarwa tsakanin shugabanin biyu dai ta faro tun a watan da ya gabata, bayan da shugaban ƙasar Viktor Yushenko ya rusa majalisar dokokin tare da kiran gudanar da sabon zaɓe gabanin waádi, lamarin da kuma P/M Yanukovic da mafi rinjayen yan majalisar dokokin suka ƙi amincewa da shi.