An kashe ´yan tawayen Taliban su 50 a kudancin Afghanistan | Labarai | DW | 22.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe ´yan tawayen Taliban su 50 a kudancin Afghanistan

Jiragen saman yakin sojojin kawance a Afghanistan sun kai harin bama-bamai kan wani kauye dake kudancin kasar inda suka halaka mutane kimanin 50. dakarun kawance dake karkashin jagorancin Amirka sun ce dukkan mutanen da aka kashen mayakan kungiyar Taliban ne, amma mazauna yankin sun ce fararen hula na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a wannan farmaki da aka kai kan lardin Kandahar dake kudancin Afghanistan. Ina tabbatar da cewa jiragen saman sojojin kawance sun kai hari kan sansanin ´yan Taliban dake kusa da kauyen Azizi dake cikin gundumar Panjwayi kuma mun yi imani an kashe ´yan Taliban sama da 50, inji kakakin sojojin kawance Manjo Scott Lundy lokacin da yake magana da kamfanin dillancin labarun AFP. Wani jami´in leken asirin Afghanistan ya tabbatarwa kamfanin AFP da kai farmakin, amma ya ce mutum 27 aka kashe.