An kashe yan gudun hijirar Sudan 10 a Masar | Labarai | DW | 30.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe yan gudun hijirar Sudan 10 a Masar

Wasu yan gudun hijira na Sudan 10 ne suka rasa rayukansu wasu 23 suka samu rauni a yau din nan a lokacinda dubban yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Masar suke neman kwantar da tarzoma da ya barke a sansanin yan gudun hijira yan Sudan dake Masar.

Shugaban masu zanga zangar Boutrous Deng,ya fadawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa,mutane 15 ne auka mutu ciki har da yara kanana.

Da sanyin safiyar yau ne yan sandan suka farwa sansanin yan gudun hijirar dake tarzoma yanzu watanni 3 ke nan .

A halin yanzu komishinan kula da yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterras,ya baiyana bakin cikinsa game da wannan mace mace,ya kuma aike da sakon taaziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka samu rauni.