An kashe yan bindiga 6 a Saudiya | Labarai | DW | 23.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe yan bindiga 6 a Saudiya

Rahotanni daga kasar Saudiya sun baiyana cewa,jamian tsaron kasar sun kashe wasu yan gwagwarmaya 6 wani dan sanda kuma ya rasa ransa a babban birnin kasar Riyadh.

Gidan telebijin na Al Arabiya ya ruwaito jamian tsaron kasar na cewa,wadannan mutane 6 suna gab da kai wani hare hare ne,wadanda baa baiyana ko wadannane iri ne ba,yayinda jamian tsaron suka far masu a maboyarsu.

Yan gwagwarmaya dai da ake ganin suna da alaka da Osama bin Laden,suna ci gaba da kokarin ganin sun kifar da gwamnatin Saudiya da Amurka ke marawa baya.

Jamian kasar sunce kimanin mutane 150 ne da suka hada da baki da kuma yan Saudiyan suka rasa rayukansu,hakazalika sojin sa kai 130,cikin hare hare da kuma arangama da yan sanda a kasar ta Saudiya tun watan mayu na 2003.