An kashe wani dan diplomasiyan Rasha a birnin Bagadaza | Labarai | DW | 03.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani dan diplomasiyan Rasha a birnin Bagadaza

Wani jami´i a ofishin jakadancin Rasha dake birnin Bagadaza ya ce an halaka jami´in diplomasiyar Rasha daya sannan aka yi garkuwa da 4 a yau asabar. Kamfanin dillancin labarun Rasha Interfax ya rawaito jami´in ba tare da ya ambaci sunansa ba, yana cewa an tabbatar da rasuwar dan diplomasiya daya sannan an sace 4. Majiyoyi daga babban birnin na Iraqi sun ce wasu ´yan bindiga a cikin motoci guda 3 sun toshe wata hanya dake shiga unguwar Mansour sannan suka bude wuta akan wata mota, inda suka kashe mutum daya kana kuma suka yi awon gaba da 4.