An kashe sojojin Faransa biyu a Afghanistan | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Faransa biyu a Afghanistan

Dakarun Afghanistan wadanda sojojin kasashe ketare ke marawa baya na ci-gaba da fafatawa da mayakan kungiyar Taliban a kudancin kasar. Sojojin Faransa biyu da wani sojin Amirka na daga cikin wadanda aka kashe a rikicin baya bayan nan. Ko da yake rahotanni sun ce an kame babban kwamandan Taliban wato Mullah Dadullah, to amma har yanzu jami´ai a Afghanistan ba su tabbatar da asalin wani gurgu da aka yiwa mummunan rauni kuma yanzu haka ya ke hannu ba. Tun a ranar laraba da ta wuce ake gwabza kazamin fada a kasar ta Afghanistan wanda yayi sanadiyar mutuwar ´yan tawaye 200 da dakarun gwamnati 25 da ´yan sanda da kuma fararen hula da dama. Wannan fadan shi ne mafi muni tun bayan hambarad da gwamnati Taliban a karshen shekara ta 2001.