An kashe sojojin Amirka guda 5 a Iraqi. | Labarai | DW | 26.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Amirka guda 5 a Iraqi.

Hukumar rundunar sojin Amirka ta tabbatar cewa ’yan yaƙin gwagwarmayar Iraqi sun kashe sojojin Amirka guda 5, a wata gwabzawar da suke ta yi tun jiya. Wata sanarwar da hukumar ta bayar ta ce dakarun rundunar mayaƙan ruwanta guda 4 da wani soja ne suka sheƙa lahira a fafatawar da ’yan wani rukunin rundunar suka yi da ’yan tawayen a jihar Al-Anbar. Wannan dai ya kawo yawan sojojin Amirka da suka rasa rayukansu a Iraqin a wannan watan zuwa 96. Kamfanin dillancin labaran nan AFP ya ƙiyasci cewa a kusan sojojin Amirka dubu 3 ne suka rasa rayukansu tun da Amirkan ta afka wa Iraqi a cikin watan Maris na shekara ta 2003.