An kashe sojojin Amirka biyu a wata fafatawa da ’yan tawayen Iraqi. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Amirka biyu a wata fafatawa da ’yan tawayen Iraqi.

Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqi, ta ce sojojinta biyu ne suka rasa rayukansu, a wata fafatawar da rukuninsu ya yi da ’yan tawaye a jihar al-Anbar da ke yammacin ƙasar. Sanarwar da hukumar ta bayar a birnin Bagadaza ta ce tun jiya asabar ne ta yi asarar sojojin, daga bataliyanta ta 13 da ke Iraqin. Sai dai ta ce ba za ta bayyana sunayen sojojin ba, sai an sanad da iyalansu tukuna. A jiya ɗin ma dai hukumar ta ce wani sojan Amirka ɗaya kuma ya mutu a wani haɗarin da motarsa ta yi a garin Mosul da ke arewacin Iraqin. Kawo yanzu dai yawan sojojin Amirka da suka rasa rayukansu a ƙasar ya kai dubu biyu da ɗari 7 da 9.