1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojoji biyu a Filato

Abdul-raheem Hassan
March 15, 2018

Rundunar sojojin Najeriya, ta tabatar da mutuwar dakarun ta biyu, a lokacin da suke kokarin kwantar da sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Filato.

https://p.dw.com/p/2uNY8
Nigeria Sicherheitskräfte Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP

Rundunar sojin Najeriyar ta ce ta tura karin wasu dakarunta a karamar hukumar Bassa, bayan samun labarin barkewar sabon tarzoma tsakanin manoma da makiyaya.

Bayan mutuwar sojoji biyu akwai wasu sojoji da suka jikkata a artabun, sabon rikicin ya zo ne kwanaki kalilan bayan wani rikici da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25 a karamar hukumar Bassa.

Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar takaita zirga-zirga a karamar hukumar Bassa daga shida na safe zuwa shida na yamma, bayan barkewar sabon rikicin.