1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojoji a Libiya

July 23, 2017

Wani sabon rikici tsakanin dakarun rundunar da ke karkashin ikon Khalifa Haftar da masu gwagwarmaya da makamai a kasar Libiya, ya halaka sojoji shida tare ma da jikkata wasu.

https://p.dw.com/p/2h1Hl
Libyen Kämpfe in Bengasi
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Alawami

Ricikin dai ya faru ne a dai dai lokacin dakarun ke kokarin dannawa zuwa sauran yankunan da mayakan tarzoma ke ci gaba da turjiya, musamman ta gabashin fadar gwamnatin kasar. Rahotanni sun kuma ce dakarun sun yi barin wuta ta sama a kan mayakan tarzoma da ke birnin Derna.

Shi dai Khalifa Haftar mayaki ne na marigayi shugaba Muammar Gaddafi da aka kashe a shekara ta 2011, wanda kuwa daga bisani ya juya masa baya. Haftar yana kuma samun goyon baya ne yanzu daga kasashen Masar da hadaddiyar daular larabawa a gwagwarmayar da ya ke jagoranta na kashin kai a Libiyar.