An kashe Shugaban kungiyar Al Qaeda a Yemen | Labarai | DW | 27.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Shugaban kungiyar Al Qaeda a Yemen

Wani jirgin kasar Amirka ya halaka jagoran Al Qaeda a Yemen.

Jirgin Amirka maras matuki

Jirgin Amirka maras matuki

Hukumomi a kasar Yemen sun tabbatar da mutuwar wani babban jagoran kungiyar Al Ka'ida da ke a kasar, wanda suka ce ya mutu ne bayan wani harin jirgin Amirka marar matuki a tsakiyar kasar. Wani babban jami'in gwamnatin Shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi, ya ce an kashe Abdallah Al Sanaani ne tare da wani dogarinsa a lokacin da suke tafiya cikin wata mota a garin Al Sawma'a dake lardin Abyan.

Kasar Amirka dai na amfani da jirage marasa matuka a Yemen, musamman wajen farautar masu kaifin kishin addini da suka haddasa yakin basasa a kasar. Jami'an Amirkar  sun kuma jima suna bayyana hadarin 'ya'yan kungiyar ta Al ka'ida a yankin gabas ta tsakiya, kungiyar da ke farwa gwamnatin kasar Yemen da bangaren 'yan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.