An kashe shugaban ƙungiyar Alqa´ida na Saudiyya. | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe shugaban ƙungiyar Alqa´ida na Saudiyya.

Ministan harakokin cikin gida na Saudiyya, ya hiddo sanarwar kashe shugaban ƙungiyar Alqa´ida na Saudiyya, Fahd Ben Faraj Ben mohamed Al Joweir.

Ya gamu da ajalinsa, ranar jiya, a sakamakon wata bata kashi, da aka yi tsakanin gungun yan ta´ada, da jami´an tsaron Saudiyya a birnin Ryad,wanda a cikin sa, mutane 4, su ka rasa rayuka.

Sauran mutanen 3 da su ka mutu, na daga jerin mutane 36, da hukumomin Saudiyya ke nema ruwa jallo.

Su na tuhumar su da hanu a hare ahren ta´adanci daban daban da su ka wakana a ƙasar, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar mutane kussan 300, daga shekara ta 2003 zuwa yanzu.

Sanarwar da hukukomin su ka bayyana, ta ce Fahd Ben Faraj, na daga ayarin, wanda su ka kitsa harin ranar juma´a, da ta wuce, inda su ka ci karro, da jami´an tsaro, a yayin da su ka buƙaci kai hari, ga wata cibiyar samar da man petur.