1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane kusan 20 a jihar Benue

Abdullahi Maidawa Kurgwi
April 24, 2018

Wasu da suka shedi lamarin sun bayyana cewar maharan sun shiga kauyen Ayar- Mbalong ne da misalin karfe shida zuwa bakwai na safiya, inda suka soma kashe-kashen mutane tare da kone gidaje.

https://p.dw.com/p/2wZNV
Nigeria Polizei
Tuni dai wasu mutane suka fara tarewa a sansanin 'yan gudun hijira saboda rikicin na BenueHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Wasu mahara da ba a tantance su ba, sun kai hari kan mazauna kauyen Ayar- Mbalong da ke karamar hukumar Gwer-East cikin jihar Benue, inda suka kashe akalla mutane 19, ciki har da wasu Limaman coci biyu. 

Basaraken gargajiya da ke kauyen Mr. Ayua Daniel Abomtse, ya tabbatar wa wakilinmu Abdullahi Maidawa Kurgwi ta wayar tarho yadda lamarin ya auku.

Kokari da wakilin mu ya yi don samun karin bayani daga rundunar 'yan sandan jihar Benue lamarin ya ci tura, to sai dai wata majiya ta ce mutanen kauyen suna kan gudu zuwa neman mafaka a kauyuka mafi kusa don tsira da rayukansu kasancewar har zuwa wannan lokacin, babu isassun jami'an tsaro a yankin.