An kashe mutane da dama a sabon fada tsakanin sojojin gwamnati da ´yan tawaye a gabashin Chadi | Labarai | DW | 05.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe mutane da dama a sabon fada tsakanin sojojin gwamnati da ´yan tawaye a gabashin Chadi

Wani fada tsakanin sojojin Chadi da ´yan tawaye da ake zargin cewa Sudan na marawa baya yayi sanadin mutuwar mutane 32 sannan sama da 50 su jikata a gabashin Chadi. Wata sanarwa daga ofishin shugaba Idris Deby ta nunar da cewa sojojin gwamnati guda 10 sun mutu sannan 17 sun samu raunuka, yayin da ´yan tawaye 22 dake samun goyon bayan gwamnatin Khartoum suka bakwanci lahira sannan 37 suka jikata a filin daga. A ranar asabar wata majiyar gwamnatin Chadi ta ce ´yan tawaye a cikin wani ayarin motoci 67 sun kai hari akan garin Tine dake gabashin Chadi a kusa da kan iyaka da Sudan, kafin daga bisani sojoji su fatattake su. Wata majiyar rundunar sojin Chadi ta ce ´ya tawayen na daukar umarni ne daga tsohon abokin dasawar shugaba Deby wato Timane Erdimi wanda ya juyawa shugaban baya a cikin watan desamban bara kuma yanzu ya zama madugun ´yan adawa.