1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane biyu a boren Nepal

April 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6q

Nepal

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a Nepal,a lokacin da yan sanda sukayi ta harbin bindiga wa masu zanga zangar adawa da masarautar gabashin kasar.Wannan ya kawo ga adadin mutane 8 kenan suka rasa rayukansu a boren makonnin biyu ,dake bukatar Sarki Gyanendra ya kafa democradiyya.A wannan zanga zangar tayau dai sama da mutane 10 ne suka jikkata a garin na Chandragadi,mai tazarar km 600 daga birnin Kathmandu,dake zama fadar gwamnati.Yan jarida da suka ganewa idanunsu wannan yamutsi dai sun sanar dacewa ,sunga gawawwakin mutane 4 da aka bindige.Tuni dai gwamnatin Nepal ta kafa dokar hana fita a garin Pokhara,dake zama wurin yawon shakatawa,dake yammacin kathmandu.A halin ake ciki yanzu haka dai gwamnati ta saki manyan yan adawa guda 2 data tsare a watanni 3 da suka gabata.Sai dai bata bada dalilin sakinsu ba.